Aikin Gyaran Kundin Tsarin Mulkin 1999 Ba Shi Da Wata Manufa Ta Boye : Sanata Barau Jibrin.

A yayin taron sauraron ra’ayoyin jama’a da ake gudanar a Kano,
Mataimakin   Shugaban   majalisar   dattawa   kuma  shugaban
kwamitin duba kundin tsarin mulki na 1999, Sanata Barau Jibrin,
ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa aikin gyaran kundin tsarin
mulki da ake gudanarwa ba shi da wata manufa ta ɓoye, kuma
yana gudana ne bisa buƙatun jama’a.

Ya bayyana cewa kwamitin ya riga ya karɓi daruruwan takardu
daga jama’a kan muhimman batutuwa kamar gyaran tsarin zaɓe
da shari’a, ’yancin kan ƙananan hukumomi da tsaro, da shigar da
mata da sarakunan gargajiya cikin tsarin mulki da batutuwan da
ba a samu daidaito a kansu ba a baya.
Mahalarta taron sun haɗa da wakilai daga jihohin Kano, Katsina,
Kaduna, Sokoto, da Jigawa.
Taron dai wanda aka so a yi ti a baya an ɗage shi domin girmama
marigayi   Alhaji   Aminu   Dantata   da   tsohon   Shugaban   Ƙasa
Muhammadu Buhari.

Post masu alaƙa

Sojoji Sun Cafke Shugaban ’Yan Bindiga A Zamfara

Yara 5 Sun Gudo Daga Hannun Boko Haram A Borno

Tinubu Ya Sha Alwashin Ceto Ɗalibai Da Malaman Da Aka Sace A Oyo Da Borno