Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kafa kwamitin bincike kan tsaya wa wani da ake tuhuma da safarar miyagun ƙwayoyi a gaban kotu da Kwamishinan Sufuri na jihar, Alhaji Ibrahim Namadi ya yi.
Wannan na cikin sanarwar da Babban Daraktan Yada Labaran gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar 26 ga Yuli, 2025.
Sanarwar ta ce matakin na gwamna ya biyo bayan bayyanar sunan kwamishinan a cikin takardun belin wani da ake zargi da laifin safarar ƙwayoyi, wanda ya tayar da kura a cikin al’umma da kafafen sada zumunta.
- Nentawe Yilwatda Ya Zama Sabon Shugaban APC
- Sojoji Sun Halaka Yan Bindiga 95 Tare Da Ceto Mutane 138 A Neja
Kwamitin da aka kafa zai kasance ƙarƙashin mai ba gwamna shawara kan harkokin shari’a, Barista Aminu Hussain, domin gudanar da bincike tare da bayar da shawarwari daidai da abin da suka gano.
Gwamna Abba ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani abu da zai zubar da kimar gwamnati ba, inda ya jaddada aniyar yaki da safarar miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka a fadin jihar.