Alhassan Ado Doguwa Ya Sake Ɗarewa Kan Kujerarsa Ta Dan Majalisar Wakilai

Hukumar zabe mai zamankata  ta bayyana Alhassan Ado Doguwa a matsayin ɗan takarar da ya lashe zaɓen ɗan majalisar wakilai daga mazaɓar Doguwa da Tudun Wada a zaben da ba a kammala ba gudanar a jiya Asabar 15 ga watan Afrilu.

An soke nasarar da ya samu a baya, a zaɓen 25 ga watan Fabrairu, saboda jami’in sanar da sakamako, Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai ya ce “tursasa masa” aka yi.

An dai sake kaɗa ƙuri’a a runfunan zaɓe 13.

 jami’in sanar da sakamako Kamala zabe na mazaɓar, Farfesa Sani Ibrahim a jiya Asabar, inda ya ayyana Alhassan Doguwa a matsayin wanda ya yi nasara bayan wannan zaɓe.

Alhassan Ado Doguwa, wanda shi ne shugaban masu rinajye a majalisar wakilai ya yi nasara ne bayan ya samu ƙuri’a 41,573, sai kuma, Yusha’u Salisu na NNPP ya samu ƙuri’a 34,831.

Dan majalisar na tarayya ya samun nasarar zuwa majalisar wakilai daga Kano tun bayan dawowar Najeriya mulkin dimokraɗiyya a 1999.

Post masu alaƙa

Jigawa Za Ta Bai Wa Alhazai Abinci Sau Uku a Rana a Hajjin 2026

Namadi Ya Kaddamar da Shirin Fadada Ilimi yayin da SLU ta Yaye Dalibai Sama da 4,000

Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Jigawa Ta Taya Gwamna Namadi Da Musulmi Murnar Eid-el-Fitr