Alhazan Najeriya 6 sun rasu a Saudiyya, sakamakon bugun zuciya

Alhazan Najeriya shida sun rasu a Saudiyya, sakamakon abin da aka bayyana a matsayin bugun zuciya.

Shugaban tawagar likitocin Najeriya mai kula da aikin hajji, Dr Usman Galadima ne ya tabbatarwa da hakan a cikin wata tattaunawarsa da manema labarai.

A cewar galadima, Galadima mahajjatan da suka rasu sun hada da biyu daga jihar Osun, sai daya  daga Kaduna da wani daya daga jihar Filato.

Ya ce, izuwa yanzu maniyyata 15,860 suka yi jinya sanadiyyar cutuka daban-daban, wadanda suka hada da mura da gyambon ciki da hawan jini da kuma cizon sauro.

inda kara da cewa sama mahajjata 100 an tura su asibitoci a kasar Saudiyya. Haka kuma wasu alhazan Najeriya 30 da aka tabbatar da cewa suna da matsalar tabin hankali an kai su asibitocin Saudiyya kuma za su yi aikin hajji saboda “yanzu suna cikin ƙoshin lafiya.

Post masu alaƙa

Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta buƙaci a biya diyyar masu haƙar ma’adinai 37 da suka rasu Neja

Atiku ya buƙaci Tinubu ya yi bayanin dalilinsa na ƙin halartar taron UNGA karo na uku a jere

Yan sanda da INEC sun yaba da yadda zaɓen Dawakin Kudu ke gudana a Kano.