Kungiyar direbobi masu dakon man fetur sun fara yajin aiki a Kasar Ghana

Kungiyar direbobin tankokin dakon man fetur a Ghana ta ce za ta fara yajin aiki a yau Litinin saboda rashin kyawun hanyoyi.

Direbobin na so ne gwamnati ta gyara hanyoyi a yankunan Tema, Takoradi da Buipe.

Sun nuna damuwa kan hadurran da ke tattare da safarar man fetur a kan hanyoyin marasa kyau.

Kungiyar yan kasuwa ta Liquified Petroleum Gas Marketers Association ta yi gargadin cewa za a iya samun karancin man LPG a kasar idan har aka shiga yajin aikin.

Post masu alaƙa

Za a miƙa ƴan Najeriya da ake zargi damfara zuwa Amurka

Ebola ta ƙara bazuwa a DR Congo

Kotun majistare ta fara sauraren shari’ar sojan gona mai mukamin CSP