Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), a ranar Talata, ta fara rabon kayan abinci da cibiyar agajin jin kai ta Sarki Salman ta bayar ga iyalai dubu 2,056 a nan jihar Kano.
Cibiyar Sarki Salman na bayar da agajin jin kai ne ga mabukata a ƙasashe daban-daban a faɗin duniya.
Shugabar hukumar NEMA, Hajiya Zubaida Umar, a lokacin da take kaddamar da rabon kayayyakin, ta ce, an yi hakan ne domin tallafa wa marasa karfi, da kuma dakile tsadar rayuwa.