Ayatullah Khamenei Jagoran Musulunci na ƙasar Iran, ya karrama kwamandan dakarun kare juyin juya hali da ya jagoranci harin makami mai linzami da ƙasar ta kai wa Isra’ila a ranar Talatar makon jiya.
Ayatullah Khamenei ya sanya wa Janar Amirali Hajizadeh aninin Fath (nasara), a ranar Lahadi da ta gabata.
Karramawar ga Janar Amirali Hajizadeh ta zo ne saboda “kyakkyawan aiki na ‘Gaskiya’”, kamar yadda shafin rundunar juyin juya halin Musulunci na Iran ta bayyana.
Janar Hajizadeh, mai shekaru 62, ya shugabanci sashin kula da sararin samaniyar rundunar sojojin Iran tun lokacin da aka ƙirƙiro ta a shekarar 2009.
Ranar Talatar da ta gabata ce dai rundunar ta harba wasu makamai masu linzami kimanin 200 kan ƙasar Isra’ila a matsayin ramuwar gayya kan harin da Isra’ila ta kai ta sama da ta yi ajalin shugaban kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah.
Wannan hari ne kuma ya yi ajalin Janar Abbas Nilforoushan, a Beirut babban birnin ƙasar Lebanon.
Wannan dai shi ne hari na biyu da ƙasar Iran ta kai wa Isra’ila kai tsaye cikin watanni shida.
Ƙasar Isra’ila ta sha alwashin mayar da martani bayan harin makami mai linzami da Iran ta kai mata a ranar Talatar da ta gabata.