Za A Dauki Matakin Doka Kan Duk Jihar Da Ba A Yi Zaben Kananan Hukumomi Ba
Gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta ce za ta ɗauki mataki a kan jihohin da suka ƙi gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi da ake sa ran zai tabbatar da cin gashin kai na ƙananan hukumomin kamar yadda kotun ƙolin ta zartar a kwanakin baya.