Trump Zai Tattauna Da Putin Don Kawo Karshen Yaki A Ukraine

Daga : Shareep Khaleepha Sharifai

Shugaban na Amurka Donald Trump ya ce zai yi magana da Vladimir Putin a ranar Talata don diga wa yakin Rasha aya.

Sanarwar tasa ta biyo bayan tattaunawar da ta nuna alamun haske ne da Trump din ya yi da jami’an Rasha a birnin Moscow.

Shugaba Trump ya fada wa manema labarai a yayin da ya ke kan hanyar komawa Washington daga Florida cewa an aiwatar da aiki mai yawa a karshen mako.

Shugaban na Amurka na kokarin shawo kan Putin ne domin amincewa da kudurin tsagaita wuta na kwana 30 da Amurkar ta gabatar wadda tuni Ukraine ta yi na’am da shi.

Post masu alaƙa

JIGAWA: ‘Yan siyasa sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya gabanin zaben 2027

Sarkin Gumel Ahmed Muhammad Sani II ya rasu

Yan sanda sun kama mutane 79 tare da kwato kwayoyi da makamai a bikin Takutaha a Kano.