M23 Ta Zargi DRC Da Yin Wasa Da Tattaunawar Zaman Lafiya

Daga : Shareep Khaleepha Sharifai

Kungiyar ‘yan tawayen M23 ta ce hare-haren da Kwango ke kaiwa kan jama’a na nuna DRC ba ta damu da a tattauna a Angola ba.

Kungiyar M23 mai samun goyon bayan Rwanda ta zargi gwamnatin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango da neman yi wa tattaunawar zaman lafiya kafar ungulu.

An dai tsara cewa za a tattauna a kasar Angola tsakanin ‘yan tawayen da kuma gwamnatin DRC da ke yakarsu a gabashin kasar bayan kwace iko da wasu manyan birane.

Mai magana da yawun M23 da kuma kungiyar Congo River Alliance ya zargi DRC da amfani da jirage maras matuka wajen yin ruwan wuta kan wuraren da ke dankare da jama’a a baya-bayan nan.

Lawrence Kanyuka ya wallafa a shafinsa na X cewa wannan farmakin na Kwango ya nuna aniyarta ta yin zagon kasa ga tattaunawar da aka jima ana neman ganin ta auku.

Shugaban kasar Angola Joao Lourenco ya bukaci a tsagaita wuta daga ranar Lahadi da dare, to amma babu wanda ya mayar da martani kan kiran nasa tsakanin DRC da M23.

Post masu alaƙa

Duk wanda ke da hannu a harin Amurka kan tsibirin Larak zai ɗanɗana kuɗarsa – Iran

An kashe kwamandojin ’yan bindiga biyu a Katsina

Yan Sandan a Kano sun kama mutane 244, ciki har da 117 da ake zargi da fadan daba.