Saudiyya za ta zuba jarin biliyoyin Dala a Siriya

Saudiyya ta sanar da wani gagarumin zuba jari a fannin samar da ababen more rayuwa a Syria, a yayin da ta ke jaddada goyon bayanta ga gwamnatin Damascus. Ƙasar Saudiyyar ta sanya kuɗin da ya kai dala biliyan biyu wajen gina sabbin filayen tashi da saukar jirage biyu a birnin Aleppo, da kuma dala biliyan […]

Read more

Shettima ya kai ziyara Kwara bayan mummunan harin jihar

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya kai ziyarar jaje zuwa jihar Kwara inda mahara suka kashe gomman mutane cikin makon nan. Cikin wata sanarwa da fadarsa ta fitar ta ce Shettima ya kai ziyarar ce bisa umarnin shugaban ƙasar Bola Tinubu. “Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya umarci mataimakinsa ya kai ziyarar jaje jihar da kuma […]

Read more

APC ta naɗa Masari shugaban babban taronta na ƙasa

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta maye gurbin gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma da tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari a matsayin shugaban kwamitin babban taronta na ƙasa. Babban sakataren jam’iyyar na ƙasa, Surajudeen Basiru ne ya bayyana haka cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X. Jam’iyyar ta saka ranakun 27 […]

Read more

Yan Jaridun Bauchi mutum 14 sun yi hatsari a bakin aiki

Tawagar ’yan jarida kimanin su 14 da suka fito daga kafafen yaɗa labarai dabam-dabam suka gamu da mummunar hatsarin mota a yayin da suke cikin tawagar Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas (NEDC). Tawagar da suke tafiya a ƙarƙashin jagorancin ƙaramin Ministan Raya Yankuna, Alhaji Uba Maigari Ahmadu a yayin da suke ziyarar buɗewa da […]

Read more