Sanata ya bar APC a jajibirin zaɓen fidda gwani a Kebbi
Sanatan Kebbi ta Kudu a Majalisar Dattawa, Garba Musa Maidoki, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC. A cikin wata wasiƙa da ya aike wa Shugaban APC na mazaɓar Rafin Zuru mai ɗauke da kwanan watan 14 ga Mayu, 2026, Sanatan ya ce ya ɗauki matakin ne sakamakon rikice-rikicen cikin gida da suka dabaibaye jam’iyyar. […]