Majalisar Najeriya ta dakatar da zuwa Afirka ta Kudu

Majalisar Dokokin Najeriya ta dakatar da wasu ziyarce-ziyarcen aiki zuwa Afirka ta Kudu, tare da cewa za ta kaurace wa duk wasu ayyukan majalisa da za su kasance a Afirka ta Kudu har zuwa wani lokaci. Matakin ya biyo bayan rahotannin kisan kai, hare-hare, tsoratarwa da lalata kadarorin da suka shafi ƴan Najeriya da sauran […]

Read more

An Kama Masu Safarar Miyagun Ƙwayoyi 7 A Jigawa

Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa ta kama wasu mutane bakwai da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, tare da ƙwato nau’in ƙwayoyi daban-daban har guda 5,916 da kuma kunshin tabar wiwi guda biyar. Kamen dai ya biyo bayan wasu samame na musamman da rundunar ta gudanar bisa bayanan sirri a wurare daban-daban na jihar, domin […]

Read more

Ebola ta ƙara bazuwa a DR Congo

Jami’ai a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo sun ce barkewar cutar Ebola ta bazu zuwa wani lardi, wanda shi ne na bakwai. Gwamnan Sud-Ubangi ya ce an tabbatar da samun cutar a yankin da ke iyaka da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Jamhuriyar Kongo. An yi imanin cewa majinyacin ya bi ta wasu larduna da dama, ciki […]

Read more

Kotun musulunci dake Jogana ta bayar da umarnin tsare mutanen da Ake tuhuma da yunkurin aikata tsafi.

Kotun shari’ar addinin musulunci dake zamanta a unguwar Jogana Kano, karkashin jagorancin mai shari’a, Kamalu Haruna, ta bayar da umarnin tsare mutanen da ake zargi da hada kai da yunkurin aikata tsafi. Wadanda ake tuhumar sun hada da, Yusuf Mahmud mazaunin Rano, Abdurraham Abbas mazaunin Kwasamgwami Gezawa da Sha’aibu Yawale Daganawa Bunkure da Abubakar Iliyasu […]

Read more