Ruwan sama mai ƙarfi ya mamaye dubban tantuna da mutanen da suka rasa matsugunansu ke zaune a cikinsu a Gaza, yayin da wani jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce kusan kowa da kowa a yankin na buƙatar agaji.
Mazauna yankin sun yi amfani da tukwane da kwanoni wajen kwashe ruwa daga tantunansu da ambaliyar ruwa ta mamaye, inda wasu suka ce yanzu ba su da wani matsuguni.
Jonathan Veitch, wakilin UNICEF a Falasɗinu, ya ce halin “matsanancin ƙunci” da ake ciki yana ƙara taɓarɓarewa sakamakon takunkumin da Isra’ila ta sanya kan shigar da manyan injuna da kayayyaki kamar man injina.
Kusan kashi 90 cikin 100 na mazauna Gaza sun rasa matsugunansu sakamakon yaƙin Isra’ila da Hamas, kuma da yawa daga cikinsu sun yi ƙaura sau da dama, tare da ƙarancin samun tsaftataccen ruwa da hanyoyin tsaftar muhalli.
Ƙungiyoyin agaji sun ce ana sa ran lamarin zai ƙara muni da zarar damina da sauka.
Da yake zantawa da BBC daga Deir al-Balah da ke tsakiyar Gaza, Veitch ya ce: “Abin yana da matuƙar muni kuma mutane sun shiga matsanancin hali.
“Muna ba da duk irin taimakon da za mu iya, amma a yanzu ma ana tare mu a kan hanya yayin da muke tafiya saboda mutane suna roƙon mu da mu taimaka musu.”
Gwamnatin Gaza da Hamas ke jagoranta ta ce kusan tantuna 70,000 ne ambaliyar ruwa ta shafa.
Wani mai magana da yawunta ya ce “rushewar daruruwan bango da rufin gidaje da suka riga suka tsage” ya jawo raunuka ga mutane, wasu daga cikinsu masu tsanani ne.
Veitch ya kuma ce an samu ƙarancin kwalta masu hana ruwa, robobin rufewa da kuma tantuna a Zirin Gaza sakamakon rage kasafin kuɗin Majalisar Ɗinkin Duniya.