Muhasa TV & Radio
Muhasa TV & Radio

Alarammomi sun amince da tsarin haɗa ilimin boko da na addini a Jigawa

Gwamnati za ta mayar da yara 5,000 makaranta a Jigawa

Ba mu ƙarƙare batun sauya kayan NYSC ba – Ministan Matasa

Rikicin Shugabanci:- Gwamnatin Kano Ta Rushe Shugabancin Hukumar Kare Hakkin Masu Siyan Kayayyaki

Mujahid Wada GuringawaOctober 26, 20250

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusif, ya rushe shugabancin hukumar kare hakkin masu siyan kayayyaki ta Jihar wato (Consumer Protection Council) dukkan su saboda ricikin shugabanci . Sakataren gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran sa ya fitar, inda ya ce […]

Read more

Rundunar Yan Sandan Kano Ta Kama Wasu Mutane Da Ake Zargin Yan Bindiga Ne A Shanono.

Mujahid Wada GuringawaOctober 26, 20250

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da cafke wasu mutane biyu da ake zargin suna da alaka da ’yan bindiga a garin Faruruwa, karamar hukumar Shanono, tare da ci gaba da kokarin da take na shawo kan matsalar rikici tsakanin manoma da makiyaya a karamar hukumar Makoda. Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP […]

Read more

Hisbah Zata Mikawa Kotu Batun Janye Auren Mai Wushirya Da Yar Guda.

Mujahid Wada GuringawaOctober 25, 20250

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta tabbatar da janye auren da ake shirin daurawa tsakanin fitaccen jarumin TikTok da barkwanci mai suna Idris Mai Wushirya da Basira ‘Yar Guda, bayan samun rahotanni dake nuna cewa akwai sabani da rashin fahimta tsakanin ɓangarorin biyu. A sakon muryar da mukaddashin babban kwamandan hisba na jihar Kano, Dr […]

Read more

Kotu Ta Daure Direban Jirgin Kasa Watanni 18 A Legas Saboda Satar Kuɗi

Mujahid Wada GuringawaOctober 25, 20250

Wata kotu a jihar Legas da ke kudancin Najeriya ta ɗaure wami direban jirgin ƙasa wata 18 a gidan yari saboda kama shi da laifin satar kuɗi. Mai Shari’a Rahman Osodi na kotun da ke Ikeja ta kama Christopher Ekene Ofielu mai shekara 39 da laifin satar naira miliyan 6.9 a ranar Litinin da ta […]

Read more

Jam’iyar ADC Ta Bukaci Shugaba Tinubu Ya Bayyana Dalilan Sauya Hafsoshin Tsaro.

Mujahid Wada GuringawaOctober 25, 20250

Jam’iyyar ADC ta nemi Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana wa ’yan Najeriya ainihin dalilin da ya sa ya sauya hafsoshin tsaron ƙasa ba zato ba tsammani. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, ya ce jam’iyyar ta damu ganin yadda aka yi sauyin ba zato ba […]

Read more

Kwastam Ta Kama Miyagun Kwayoyi Na Sama Da Naira Miliyan 5 A Legas

Mujahid Wada GuringawaOctober 25, 20250

Hukumar Kwastam ta Nijeriya ta kama miyagun kwayoyin da aka kimanta darajarsu zuwa Naira millyan ɗari biyar da sittin da biyu a yankin Gbaji na Badagryn  Jihar Legas. An gano kwayoyin ne a lokacin wani aikin bincike da jami’an Zone A, Ikeja, suka gudanar a kan hanyar da ta kai iyakar Seme. Kwamandan Sashen, Mohammed […]

Read more

Sauke Hafsoshin Tsaro: Za A Yi Wa Janar-Janar 60 Ritaya Daga Aiki

Mujahid Wada GuringawaOctober 25, 20250

Rundunar Sojin Najeriya za ta fuskanci babban sauyi wanda zai tilasta wa manyan sojoji yin ritaya daga aikinsu. Rahotanni sun bayyana cewar akalla Janar-Janar 60 ne ake sa ran za su yi ritaya sakamakon sabbin sauye-sauye da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa Hafsoshin Tsaro. Sanarwar da aka fitar a ranar Juma’a ta tabbatar […]

Read more

Al’ummar Shendam Sun Zargi Yan Sanda Da Taimakawa Yan Daba Wajen Rushe Musu Gidaje.

Mujahid Wada GuringawaOctober 25, 20250

Mazauna unguwar Tudun Wada da ke garin Shendam a Jihar Filato sun zargi wasu jami’an ’yan sanda da ba wa ’yan daba kariya wajen rusa gidajensu. Shaidu sun ce sama da ’yan sanda 100 ɗauke da makamai ne suka isa yankin da misalin karfe 5 na safiyar Laraba, suka ba wa wasu ’yan daba kariya […]

Read more

Yadda Yan Bindiga Daga Katsina Suke Yi Wa Mazauna Shanono Barazana Da Satar Dabbobi A Kano

Mujahid Wada GuringawaOctober 25, 20250

Mazauna yankin ƙaramar hukumar Shanono da ke jihar Kano sun koka game da yadda ‘yanbindiga ke kai musu hare-hare tare da sace mutane da dabbobinsu. A ranar Alhamis ne wata ƙungiyar mazauna ta yi taron manema labarai domin shaida wa duniya yadda suka ce ‘yan bindigar na tsallakawa daga Katsina domin kai musu hare-hare. Yayin […]

Read more

Gwamna Namadi Ya Jaddada Aniyar Sa Ta Daƙile Cutar Tamowa a Jihar Jigawa

Muhammad Auwal SuleimanOctober 25, 20250

Gwamnan Jigawa Malam Umar Namadi ya ƙaddamar da wani kwamati daga cikin majalisar zartarwar Jihar wanda zai kula da harkokin abinci mai gina jiki da ake wa laƙabi da “nutrition 774”.

Namadi ya Jaddada aniyar sa ta daƙile matsalar tamowa da kuma inganta samar da abinci a fadin Jihar. 

Read more

Posts navigation

1 … 82 … 278
View Desktop Version

Wanda ya kera Maestro Solutions

Koma Sama