Sauke Hafsoshin Tsaro: Za A Yi Wa Janar-Janar 60 Ritaya Daga Aiki

Rundunar Sojin Najeriya za ta fuskanci babban sauyi wanda zai tilasta wa manyan sojoji yin ritaya daga aikinsu.

Rahotanni sun bayyana cewar akalla Janar-Janar 60 ne ake sa ran za su yi ritaya sakamakon sabbin sauye-sauye da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa Hafsoshin Tsaro.

Sanarwar da aka fitar a ranar Juma’a ta tabbatar da sauke Janar Christopher Musa daga mukaminsa na Babban Hafsan Tsaro tare da wasu hafsoshi.

Janar Laftanar Olufemi Oluyede, wanda a baya shi ne Babban Hafsan Sojin Kasa, shi ne yanzu sabon Babban Hafsan Tsaro.

Janar Meja Waidi Shaibu shi ne sabon Babban Hafsan Sojin Kasa, yayin da Air Vice Marshal Sunday Kelvin Aneke, ya zama sabon Babban Hafsan Rundunar Sojin Sama.

Hakazalika, Rear Admiral Idi Abbas, ya zama Babban Hafsan Rundunar Sojin Ruwa, yayin da Janar Meja E.A.P. Undiendeye ya ci gaba da rike mukaminsa na Babban Hafsan Rundunar Leken Asiri ta Tsaro.

Majiyoyi daga rundunar soji, sun bayyana cewa wannan sauyi zai yi sanadin ajiye aikin manyan jami’an da suka fi sabbin hafsoshin matsayi, kamar yadda tsarin aikin soji ya tanada.

Wata majiya ta ce: “Da zarar an rantsar da sabbin hafsoshin, wadanda da suka fi su matsayi za su yi ritaya.”

Rahotanni sun ce jami’an da abin zai shafa sun fito ne daga tawagar da suka yi kwas na 38, 39 da kuma wasu daga tawaga ta 40 na Makarantar Horon Sojoji ta NDA.

A cewar majiyoyi, yana cikin tsarin aikin soji na tabbatar da ladabi, bin doka, da kiyaye tsarin mulki na rundunar.

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa an dauki matakin ne domin inganta harkar tsaro da kuma inganta hadin kai tsakanin bangarorin rundunonin tsaro.

Sabbin nade-naden na zuwa ne kwanaki kadan bayan jita-jitar yunkurin yin juyin mulki da ta karade kafafen yada labarai.

Sai dai babu wata hujja da ta nuna cewa wadannan rahotanni na da nasaba da sabbin nade-naden.

Masana harkokin tsaro sun bayyana cewa yi wa manyan jami’ai ritaya zai bai wa sabbin kwamandoji matasa damar su jagoranci rundunonin tsaro, lamarin da ka iya kawo sabon sauyi a harkar tsaro.

Tsohon mai magana da yawun rundunar sojin kasa, Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka (mai ritaya), ya bayyana cewa matakin da aka dauka abu ne da aka saba gani a tsarin aikin soja.

A cewarsa, sauyin shugabanci kan kawo sabbin dabarun aiki.

A wata sanarwa da hadimin shugaban kasa, Sunday Dare, ya fitar, fadar shugaban kasa ta yaba wa tsofaffin hafsoshin bisa sadaukarwarsu da kishin kasa, inda ta bayyana cewa sabbin nade-naden na daga cikin kokarin gwamnatin Tinubu na inganta tsarin tsaron kasa da tabbatar da zaman lafiya.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda