Hisbah Zata Mikawa Kotu Batun Janye Auren Mai Wushirya Da Yar Guda.

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta tabbatar da janye auren da ake shirin daurawa tsakanin fitaccen jarumin TikTok da barkwanci mai suna Idris Mai Wushirya da Basira ‘Yar Guda, bayan samun rahotanni dake nuna cewa akwai sabani da rashin fahimta tsakanin ɓangarorin biyu.

A sakon muryar da mukaddashin babban kwamandan hisba na jihar Kano, Dr Mujahedeen Aminudden Abubakar ya aike wa manema labarai ranar asabar, ya ce bayan gwaje gwajen da suka yi, wadanda ake shirin daura wa auren sunce, babu wata soyayya a tsakaninsu kawai sun amsawa kotu bada son ran su ba.

Hukumar hisbar ta ce bisa abubuwan da suka gano na rashin fahimtar tsakanin mai Wushirya da kuma Yar-guda an janye batun auren, kuma za a mayar da su kotu don ta bayyana matsayar ta.

Ya kara da cewa hukumar ta ɗauki wannan mataki ne domin gujewa rikici da kuma tabbatar da cewa auren ya kasance cikin yardar juna da fahimtar duka masu ruwa da tsaki.

Rahotanni sun ce Hisba ta shiga lamarin ne bayan da aka samu ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta kan yadda aka tsara bikin, tare da zargin cewa wasu bayanai sun saba da ƙa’idojin aure na addinin Musulunci.

Tunda farko ana zarginsu da yada wasu faifayen bidiyo na rashin da’a a shafukan sada zumunta.

Post masu alaƙa

Dubun masu ƙera muggan makamai a Filato ta cika

Dalilin da ya sa na gina Masallatai 50 da aurar da marayu 10 — Mataimakin Gwamna

Dalilin da ya sa zan yi takara – Yusuf Buhari