Al’ummar Shendam Sun Zargi Yan Sanda Da Taimakawa Yan Daba Wajen Rushe Musu Gidaje.

Mazauna unguwar Tudun Wada da ke garin Shendam a Jihar Filato sun zargi wasu jami’an ’yan sanda da ba wa ’yan daba kariya wajen rusa gidajensu.

Shaidu sun ce sama da ’yan sanda 100 ɗauke da makamai ne suka isa yankin da misalin karfe 5 na safiyar Laraba, suka ba wa wasu ’yan daba kariya yayin da suke lalata gine-ginen jama’a

Lamarin ya jawo zanga-zangar da mazauna yankin, ciki har da mata da yara, suka gudanar don nuna adawa da abin da suka kira “cin zarafi daga jami’an tsaro.”
Mazaunan sun bayyana cewa rushewar gidajen ta faru ne da haɗin gwiwar iyalan Fuanter duk da cewa ana shari’a a gaban kotun ɗaukaka ƙara kan mallakar filayen.

Sun ce suna da takardun mallaka, kuma sun daɗe suna zaune a wurin ba tare da wata matsala ba.
A cewar su, irin wannan yunƙurin rusa gidajen ya taba faruwa a shekarar 2023, sai dai Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan Sanda (DIG) na yankin ya dakatar da lamarin bayan ƙorafe-ƙorafen da ke zargin tsohon Kwamishinan Kasa da Tsare-tsare na Jihar Filato, Mista Festus Fuanter, da jagorantar aikin — abin da ya musanta, yana mai cewa rikicin tsakanin iyalansa ne da wasu mutum uku.

Wani mazaunin yankin, Muhammadu Bashiru, ya ce: “Da asubahin Laraba misalin karfe 5:45 na safe muka ga motoci Hilux guda shida ɗauke da ’yan sanda da ’yan daba suka fara rusa gidajenmu. Sun ƙona wasu gine-gine, sannan suka zuba wani sinadari mai guba a wasu wurare.”

Shi ma wani da abin ya shafa, Abbass Tega, ya ce an yi rusau ɗin ba tare da wata umarnin kotu ba kuma babu jami’in kotu da ya halarci lokacin da abin ke faruwa.

Ya ƙara da cewa Shugaban Ƙaramar hukumar Shendam yana ƙoƙarin sasanta rikicin kafin jami’an su dawo da rushe-rushen a wannan makon.

Da aka tuntube shi ta waya, Mista Fuanter ya ce ba shi da hannu a ƙarar da ke kotu, kuma kotun faukaka ƙara ta riga ta yanke hukunci, yayin da waɗanda suka kai kara suka kasa ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli.

Kakakin ’yan sandan Jihar Filato, DSP Alabo Alfred, ya tabbatar da samun labarin lamarin, yana mai cewa rundunar ta fara bincike kan abin da ya faru

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda