Amurka Ta Soke Bizar Wole Soyinka

Fitaccen marubucin adabin nan ɗan Najeriya, Wole Soyinka, ya ce a bara Amurka ta dauki matakin kwace takardunsa na izinin shiga kasar.

Mawalafin – wanda a shekarar 1986 ya lashe lambar yabo ta Nobel ɓangaren adabi – ya ce yanzu Amurkar ta soke takardun nasa domin haramta masa shiga ƙasar.

Wole Soyinka ya ce Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya nemi ya miƙa fasfo ɗinsa na tafiye-tafiye, domin a kammala ɗaukar matakin sokewar.

Sai dai ya sanar da cewa ba shi da masaniya kan wani mummunan laifi da ya aikata da har zai sa Amurkan ta soke bizar da ta ba shi.

“Ya zama dole ne na kira wannan taron saboda mutanen Amurka da ke tsammanin zuwana wasu taruka da cewa kar su ɓata lokacinsu.

“Ba ni da biza; an haramta min shiga Amurka. Saboda haka idan kuna son ganina, kun san inda za ku same ni,” in ji Soyinka.

“Har yanzu ina bibiyar tarihina na baya… Ba ni da wani tarihin aikata laifuka a baya ko ma babban laifi ko rashin ɗa’a da zai sa in cancanci a soke min biza.

“Na fara waiwayen baya—shin na taɓa yi wa Amurka wani rashin adalci? Shin ina da wani mugun tarihi? An yanke min hukunci? Shin na saɓawa wata doka a ko’ina?”

Marubucin dai ya taɓa koyarwa a wasu daga jami’o’in ƙasar kimanin shekara 30 a baya.

Kuma har kawo yanzu ofishin jakandin Amurkar da ke Najeriya bai ce kome ba akan batun.

Related posts

Tinubu Ya Cire Sunan Maryam Sanda Daga Waɗanda Ya Yi Wa Afuwa

Ba Daidai Ba Ne Tinubu Ya Ci Gaba Da Ciyo Bashi Duk Da Cire Tallafin Mai – Sanusi

Yan Sanda Dubu 45,000 Ne Za Su Kula Da Zaben Jihar Anambra