Daga Hassan Abdu Mai Blouse
Kwamitin zaman lafiya na jihar Kano ya yi kira da kada a shiga zanga-zangar tsadar rayuwa irin wadda aka shiga a baya kamar yadda ake raɗe-raɗi.
Kwamitin zaman lafiya na jihar Kano ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya gudanar ƙarƙashin Jagorancin shugaban sakatariyar Amb. Ibrahim Waiya.
Kwamitin zaman lafiyar ya ja hankalin masu shirya wannan zanga-zangar kamar yadda ake raɗe-raɗi inda yace
“babu wani Ɗa mai ido da zanga-zangar da aka gudanar a baya ta haifar face asarar dukiyoyi ta gwamnati dama wanda basu ji – basu gani ba, musamman idan aka duba abinda ya faru a jihar Kano yadda wasu da ake zargi marasa kishin ƙasa sunyi amfani da wannan damar wajen tura yara wanda basa kishin jihar suka afkawa kayan gwamnati dama ƴan kasuwa”.
- Ce-Ce ku-Ce ya Ɓarke Tsakanin Sojoji Da Jama’ar Kaduna
- Kashi 40 Na Ƴan Najeriya Na Samun wutar Lantarki Na Awa 20 A kullum – Gwamnati
Ambasada Waiya ya ce a kwai hanyoyin kiranye ga shugabannin da al’umma suke ganin sun gaza wajen kare muradun su da kawo musu canji wanda kudin tsarin mulkin ƙasa ya tanada, ya kuma bai wa masu zaɓe damar aikata hakan a duk sanda suke ganin ya kamata.
A ƙarshe, Ambasada Waiya ya tabbatarwa al’umma musamman na jihar Kano cewa babu Kano a jerin wuraren da ake shirin shiga wannan zanga-zangar tsadar rayuwa da wasu ke yunkurin shiryawa.