Ɗan Malikin Sarkin Hausawan Maraban Gurku ya yi kira ga matasa su kai zuciya nesa, malamai kuma su ƙara kaimi wajen isar da sakon halin da talakawa ke ciki ga shugabanni.
Malam Muhammad Mubarak Jalo, Danmalikin Sarkin Hausawan Maraban Gurku, kuma Danmalikin Sarkin Hausawan Juwape, ya bayyana hakan ne a tattaunawar sa da gidan rediyon Muhasa.
Ya ce, a kwai tambayoyin da ya kamata shugabanni su amsa dangane da matsalolin da Najeriya ke fuskanta.
Ya ce, “matsalolin daga shugabanni ne, shiyasa mutane suke shirin nuna bacin ransu. bayan bata lokaci wajen jefa kuri’a amma har yanxu bata canja zani ba,ita dimokuraɗiyya tsari ne na hidimtawa alumma.”
- An kafa kwamiti Kan Sabon Mafi ƙarancin Albashi A Kano
- APC Ta Zargi Masu Zanga-zanga Da Niyyar Kifar Da Gwamnatin Tinubu
Muhammad Mubarak Jalo yace malamai suna iya kokarin su, kuma suna bada gudunmawa wajen gyaruwar alumma, saidai akwai bukatar su zage damtse don isar da sakon talakawan kasar ga shugabanni.
“kamata yayi mamalamai su matsa lamba wajen nusar da shugabanni halin da mutane ke ciki.”
A tsokacin da yayi game da shirin zanga -zangar da matsa ke yi, Danmaliki ya bayyana cewa a farko yana goyon bayan zangar zangar amma yanxu ya sauya ra’ayinsa.
“A farko a matsayina na matashi ina goyon bayan zanga zanga, amma a halin yanxu ina ganin ya kamata a hakura domin dalilai na tsaro da zaman lafiya, abin da ya kamata ayi shine a nemi wata maslahar, kasashe da yawa sun rasa zaman lafiyar su saboda barkewar zanga-zanga, amma ya kamata shugabanni su sani cewa, matsalar nan idan ta tashi ba iya talakawa za ta shafa ba, a’a har su”
Basaraken ya ce, yana ganin matasa basa samun abin da ya kamata, na daga kayan more rayuwa, hakan yasa suke son nuna bacin ransu.
“Dole matasa suyi bore domin shugabanni basu nema musu mafita ba, dan talaka bashi da makoma, ina ganin matasa suna da hujjar yin zanga zanga, sai dai akwai bara gurbi wanda zasu iya shiga dan kawo wata manufa da zata haifar da tashin hankali a kasar.”
A karshe yayi kira ga matsa da suyi hakuri, kuma su jajirce wajen zaɓar ‘yan uwansu matasa domin share musu hawayensu.
“Ina kira ga matasa suyi hakuri, su kuma shugabbanni suji tsoron Allah, su sani cewa, Allah yana madakata, akwai bukatar matasa su hada kansu domin tsayar da ‘yan uwansu matasa takara wanda suka san matsalarsu.
“Shugaban kasar senegal misali ne na irin yadda matasan shugabanni ke aiki don cigaban kasar su.
“Ya kamata Shugabanni suyi koyi da mazan jiya irinsu Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa, Sir Ahmadu Bello Sardauna da sauransu wajen kishin kasa”
Basaraken ya ce, ya kamata mahukunta su duba su gyara, matasa kuma su yi hakuri ayi ta addu’ a sannan a dage wajen fita takara domin matashi shima zai iya zama ɗan majisa ko kuma shugaban kasa.