Dan gwagwarmaya kuma tsohon ministan matasa da wasanni, Barista Solomon Dalung ya bayyana cewa za su fara zanga-zanga a yau Alhamis saboda su nuna fushinsu kan yadda ake tafiyar da lamurra a Najeriya.
Barista Solomon Dalung ya tabbatar da cewa zanga-zangar da za su fara ta lumana ce.
Tsohon ministan ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da kafar yada labarai ta BBC Hausa.
- An Buƙaci Matasa Su Kai Zuciya Nesa
- APC Ta Zargi Masu Zanga-zanga Da Niyyar Kifar Da Gwamnatin Tinubu
Dalung ya ce zanga-zanga ce kadai yaren da gwamnati ke ji
“wannan ne yaren da gwamnati ke ganewa kadai.”
Kawo yanzu dai matasan Najeriya sun dage kan aniyarsu ta gudanar da zanga-zangar da suke cewa itace hanyar da za su bi domin bayyanawa gwamnati halin da suke ciki.