Shugabannin jam’iyyar APC a jihohi 36 na Najeriya da kuma babban birnin tarayya Abuja, sun ce ba za su naɗe hannu suna gani a kifar da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da sunan zanga-zanga ba.
Da yake yi wa manema labarai jawabi a sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa a ranar Litinin a Abuja, shugaban jamiyyar APC reshen jihar Kuros Riba kuma sakataren kungiyar Ciyamomin jam’iyyar a jihohi, Alphonsus Ogar Eba (esq), ya ce zanga-zangar ta kwanaki 10 da aka shirya, wani yunkuri ne na neman kifar da gwamnatin Tinubu.
Alphonsus Ogar Eba (esq) ya yi wannan jawabi ne a gaban shugabannin jamiyyar da suka fito daga jihohi 36 da Abuja, a wani yanayi da ke nuna goyon bayansu ga matsayar da ya bayyana.
A safiyar yau Litinin dai rahotanni sun tabbatar da cewa an kaddamar da zanga-zangar adawa da yunwa da tsadar rayuwa a jihar Neja.