An Ceto Mutane 9 Daga Haɗarin Kwale-kwale A Sokoto

Hukumomi a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya sun ce mutum ɗaya ya rasu, sannan an ceto wasu daga haɗarin kwale-kwale da ya auku a jihar.

Haɗarin ya auku ne a ranar Alhamis a ƙaramar hukumar Shagari, inda fasinjojin cikin kwale-kwalen da dama suka ɓace kafin a bazama neman su.

Mai taimaka wa gwamnan jihar, Ahmed Aliyu a hukumar agajin gaggawa ta jihar SEMA, Aminu Bodinga ne ya tabbatar wa tashar Channels ta faruwar lamari.

Rahotanni sun ce a sanadiyar agajin gaggawa ta hukumar NEMA da SEMA ta jihar da sauran takwaororinsu tare da haɗin gwiwa ƴan garin ne aka samu nasarar ciro gawar wani mai shekara 29.

Haka kuma an samu nasarar ceto mutum, a daidai lokacin da ake ci gaba da neman wata dattijuwa mai shekara 80.

Wannan kifewar kwale-kwalen ita ce ta uku da aka yi a jihar Sokoto a cikin mako biyu bayan na ƙauyen Kojiyo da ke ƙaramar hukumar Goronyo da kuma wanda ya auku a ƙauyen Garin-Faji da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni.

Post masu alaƙa

Gwamnatin Jigawa ta kashe kusan naira biliyan bakwai (7) domin tallafa wa ma’aikata ta fuskar noma

Jami’an tsaro sun ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Kogi

Hukumomin tsaro sun kama wanda ya kirkiri hukumar bogi a Nijeriya