An cire Najeriya Daga Jerin Kasashe Na FATF Masu Halasta Kuɗin Haram

An cire Najeriya da Afirka ta Kudu daga jerin kasashen da aka fi saka wa ido saboda yawan aikata zamba da kuma halasta kuɗaɗen haram a duniya.

Ƙungiyar kula da irin waɗannan laifuka ta Financial Action Task Force (FATF) mai hedikwata a Faransa ta bayar da sanarwar cire ƙasashen biyu mafiya girman tattalin arziki a Afirka yau Juma’a bayan taronta.

Ta kuma cire ƙasashen Burkina Faso da Mozambique daga jerin nata na ƙasashen da take bayar da shawarar tsaurara saka ido a kan su saboda ayyukan masu damfara da halasta kuɗin haram.

A shekarar 2023 ne aka saka Najeriya da Afika ta Kudu ciki jerin, kuma FATF ta ce Najeriya ta ƙarfafa wa hukumomi gwiwar yin aiki tare.

Wata sanarwa daga fadar shugaban Najeriya ta ce Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana matakin a matsayin “gagarumin cigaba a yunƙurin Najeriya na gyaran tattalin arziki da kuma inganta ayyukan ma’aikatun gwamnati”.

Post masu alaƙa

AIG Garba Ahmed ya bukaci daliban Sakandaren ’Yan Sanda Dawakin Kudu su zama jakadu na gari.

Babu ɗaga ƙafa tsakanin mu da masu sha da dillancin miyagun ƙwayoyi a Kano – Anti-Phone Snatching Force.

Kwamitin yaki da shaye-shaye da fadan daba na Kano ya nemi hadin kan hukumomin tsaro