Gwamnan Bauchi Ya Naɗa Dan Uwansa A Matsayin Sabon Sarkin Duguri

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya naɗa babban ɗan uwansa, Alhaji Adamu Mohammed, a matsayin sabon Sarkin Masarautar Duguri.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Aminu Hammayo ne, ya bai wa sabon Sarkin takardar naɗin a madadin gwamnan, a wani biki da aka gudanar a fadar sarkin Duguri, da ke Ƙaramar Hukumar Alkaleri, a ranar Juma’a.

A yayin bikin, Sakataren Gwamnatin Jihar, ya shawarci sabon Sarkin da ya ci gaba da mara wa manufofi da shirye-shiryen gwamnati baya, domin samar da ci gaba mai ɗorewa a jihar.

A nasa jawabin, sabon Sarkin Duguri, Alhaji Adamu Mohammed, ya gode wa Gwamna Bala Mohammed bisa wannan karamci.

Ya yi wa ɗan uwan nasa addu’ar Allah Ya saka masa da alheri.

Ya kuma yi alƙawarin yin biyayya ga Gwamnatin Jihar Bauchi da kuma Majalisar Masarautar Bauchi.

Hakazalika, Hammayo, ya miƙa wa sabon Sarkin masarautar Bununu, Alhaji Jibrin D. Hassan, takardar naɗinsa.

Ya shawarce shi da ya yi aiki bisa doka da oda, tare da tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin ƙabilu daban-daban a yankinsa.

A nasa martanin, sabon Sarkin Bununu, ya gode wa gwamnan bisa amincewa da shi, tare da tabbatar da cewa ba zai bai wa gwamnati da al’umma abin kunya ba.

Gwamna Bala Mohammed, ya rattaba hannu kan dokar da ta ƙirƙiro sabbin masarautu 13 a Jihar Bauchi.

Post masu alaƙa

AIG Garba Ahmed ya bukaci daliban Sakandaren ’Yan Sanda Dawakin Kudu su zama jakadu na gari.

Babu ɗaga ƙafa tsakanin mu da masu sha da dillancin miyagun ƙwayoyi a Kano – Anti-Phone Snatching Force.

Kwamitin yaki da shaye-shaye da fadan daba na Kano ya nemi hadin kan hukumomin tsaro