A daidai lokacin da ake zanga-zangar tsadar rayuwa a sassa daban-daban na Najeriya, wasu sun fito kan manyan titunan jihar Kano domin nuna goyon baya ga salon mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Mutanen sun fito ne ta titin Audu Bako da kuma Farm Centre suna bayyana adawa ga abin da suka kira zanga-zangar neman tashin hankali.
Magoya bayan shugaba Tinubu sun yi taro a Fadar Sarkin Kano da ke Nasarawa, gidan da sarki Aminu Ado ke zaune.
Yayin zaman nasu a fadar sarki Aminu Ado,sun saurari jawabai kan hanyoyin da za a magance matsalolin da ke addabar kasar.
Daya daga cikin jagororin bangaren da ke yabawa shugaba Tinubu Abdullahi Muhammad Saleh ya ce , “Mun fito domin yaba ayyukan cigaban da Shugaba Bola Tunubu ya aiwatar.
“Muna jinjina masa da ya kafa Hukumar Kula da Cigaban Arewa Maso “Mu dai muna goyon bayan wannan gwamnati saboda mun san abubuwan da take yi.”