Home » An Harbe Dan Fashi An Kwato Bindigogi 7 A Wurinsa A Abuja

An Harbe Dan Fashi An Kwato Bindigogi 7 A Wurinsa A Abuja

Rundunar ’yan sanda sun samu nasarar harbe wani dan fashi inda suka kama abokansa da bindigogi bakwai a Maitama da ke Abuja.

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Rundunar ’yan sanda sun samu nasarar harbe wani dan fashi inda suka kama abokansa da bindigogi bakwai a Maitama da ke Abuja.

Ajoa Adewale, kwamishinn ’Yan Sanda na Babban Birnin Tarayya, ya bayyana hakan ne a safiyar Talata.

Ya ce rundunar ta kama gungun wasu mutum bakwai da suka kware wajen aikata fashi d makami da kuma kwacen motoci a birnin na Abuja. 

Da ya ke bayyana yadda abin ya faru, Ajao ya ce ’yan fashin suna ganin ’yan sanda suka bude musu wuta, inda jami’an suka yi nasarar harbe wani wanda aka fi sani da Baballe, suka kama wasu guda bakwai. Shugaban ’yan fashin, wanda ake kira Pastor Mogu da wani mutum daya sun tsere da raunin harbi a jikinsu.

Abubuwan da aka kwace a hannun ’yan fashin sun hada da bindigogi kirar AK-47 guda hudu, pistol kirar gida guda biyu da wata babbar bindiga da harsasai. Sauran sun hada da mota kirar Toyota Corolla da kuma babur kirar Boxer.

Kwamsihinan ’yan sandan ya ce mutum biyu daga cikin ’yan fashin, tsoffin fursunoni da wani wanda ’yan sanda suke nema bayan ya tsere daga inda ake tsare da shi a Jihar Bauchi.

Ya ce, an samu nasarar ne a wani samame da jami’an runduna ta musamman masu aikin ya ki da miyagun laifuka suka kaddamar.

Rundunar a cewarsa, ta dade tana hakon gungun ’yan fashin da suka addabi mutane da kwacen motoci.

Bayan samun rahoto shirinsu na fara aiki a unguwar Maitama ne jami’an rundunar suka shammace su.

Ajao ya ce ana ci gaba da bincike kuma da zarar an kammala za a gurfanar da su a gaban kuliya domin su fuskanci hukunci

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?