An kama matashin da ake zargi da satar baburan Adaidaita Sahu ta hanyar amfani da bandejin karya.

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wani matashi mai suna Muhammad Sani, da ake zargi da satar baburan adaidaita sahu ta hanyar yin kamar ba shi da lafiya, inda yake nade kafarsa da bandeji.

Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce matashin kan shiga adaidaita Sahu da bandeji a kafarsa, daga nan ya roƙi direban ya tsaya ya sayo masa wani abu, amma kafin ya dawo sai ya gudu da babur din.

Ya ce an kama shi ne bayan rundunar ta samu korafe-korafe guda biyar, bisa umarnin kwamishinan ’yan sandan jihar Kano , CP Ibrahim Adamu Bakori.

Binciken ya kuma kai ga kama Aminu Sa’idu, wanda ake zargi da sayen baburan da aka sace, inda aka kwato babura guda huɗu.

Rundunar ta ce waɗanda ake zargin za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.

Post masu alaƙa

Atiku ya naɗa El-Rufai cikin mambobin kwamitin yaƙin zaɓensa

Yara mata 4 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa

Ba na jin haushin abokaina da suka yi shiru kan tsare ni — El-Rufai