CP Bakori ya umarci kwamandojin yan sanda su ƙara kaimi wajen yaki da laifuka a Kano.

 

Kwamishinan yan sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya umarci dakarun rundunar da su

ƙara kaimi wajen yaki da miyagun laifuka.

CP Bakori ya bayar da umarnin ne , a hedikwatar ’yan sanda ta jihar da ke Bompai, a ranar Litinin.

Ya ce jami’an su ci gaba da yin amfani da sahihan bayanan sirri, tare da kara inganta aikin tsaro da al’umma da sarakunan gargajiya, da kuma sauran masu ruwa da tsaki.

Kwamishinan ya kuma bukaci jami’an da su riƙa amsa kiran gaggawa neman agaji akan lokaci tare da mutunta haƙƙin bil’adama.

Ya gargadi jami’an cewa rundunar ba za ta lamunci cin hanci da rashawa, rashin da’a ko take haƙƙin bil’adama ba.

Bakori ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa ’yan sanda haɗin kai, tare da sanar da su bayanan da za su taimaka wajen kare rayuka da dukiyoyinsu.

Post masu alaƙa

KACRAN: Babu wani babban rikicin manoma da makiyaya a Yobe

CP Ibrahim Bakori ya kai gaisuwar ban-girma ga Sarkin Karaye tare da halartar bikin rantsar da yan NYSC.

Yan Sanda Sun Kama Ɓarayin Wayar Lantarki A Katsina