• Home  
  • An Kama Mutum 1 Saboda Kashe Dogarin Sarki Sanusi Na 2
- Babban Labari - Labarai

An Kama Mutum 1 Saboda Kashe Dogarin Sarki Sanusi Na 2

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya reshen jihar Kano ta ce ta kama wani da take zargi da kashe wani jami’in tsaron Sarkin Kano Na 16 Malam Muhammadu Sanusi yayin aikin sa-kai a filin Idi.

Gwamnan Kano Mai Jiran Gado Ya Gayyaci Sarki Muhammadu Sanusi II Bikin Rantsuwa

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya reshen jihar Kano ta ce ta kama wani da take zargi da kashe wani jami’in tsaron Sarkin Kano Na 16 Malam Muhammadu Sanusi yayin aikin sa-kai a filin Idi.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce wani matashi mai shekara 20 ne ya daɓa wa jami’in wuƙa yayin da yake aikin kare tawagar Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II bayan sallar Idin Ƙamar Sallah da aka gudanar da safiyar ranar Lahadi.

Wani rahoto da kafar yaɗa labarai ta BBC Hausa ta wallafa ya ce, an ji wa wani jami’in sa-kai ɗin rauni kuma yana jinya a asibitin Murtala Muhammad da ke ƙwaryar birnin Kano.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan Sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Kiyawa ya bayyana cewa “Rundunar ta fara bincike kan lamarin, har ma ta gayyaci Shamakin Kano Alhaji Wada Isyaku domin amsa tambayoyi,”

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai