Hukumar tsaro ta sibil difens (NSCDC) ta sanar da cafke wani mutum, Salisu Muhammad, mai shekaru 45, bisa zargin kashe jami’inta, Bashir Adamu Jibrin, a kasuwar Shuwarin da ke Karamar Hukumar Kiyawa a Jihar Jigawa.
A cewar wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Muhammed Badarudeen ya fitar a Dutse, babban birnin jihar, lamarin ya faru ne a ranar cin kasuwar Shuwarin lokacin da marigayin yake bakin aiki.
Rahotanni sun nuna cewa, ana zargin Salisu ya buga wa jami’in dutse a kai, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.
Hukumar ta ce ta kama wanda ake zargin ne a gidansa da ke Shuwarin a ranar 7 ga watan Agusta, 2025.
Sai dai bayanai sun ce Salisu wanda bai cimma nasara ba yayi ƙoƙarin tserewa a yayin da ake jigilar sa zuwa hedikwatar NSCDC da ke Dutse a cikin motar jami’an tsaron.
- Kungiyar ACF Ta Bukaci Hadin Kan Mahukunta Don Magance Matsalolin Arewacin Nijeriya
- Gwamnan Kano Ya Kori Masu Taimaka Masa Na Musamman Guda 2
Sanarwar ta ƙara da cewa, Salisu ya samu raunuka ne yayin da yake ƙoƙarin tserewa, kuma daga bisani aka kai shi babban asibitin Dutse, inda aka tabbatar da rasuwarsa sakamakon raunikan da ya samu.
Sai dai ’yan uwansa sun buƙaci cikakken bayani dangane da raunikan da ya samu har da dalilin rasuwarsa a asibitin Sambo Limited wanda aka garzaya da shi bayan ya yi yunƙrin tserewa daga mota da ke tafe.

