Gwamnan Kano Ya Kori Masu Taimaka Masa Na Musamman Guda 2

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta amince da korar wasu manyan ma’aikata na musamman (SSAs) nan take bayan rahoton kwamitocin bincike.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Alhaji Umar Farouk Ibrahim ya fitar da safiyar Asabar.

Gwamnan ya kori Abubakar Umar Sharada, babban mataimaki na musamman kan harkokin siyasa, bayan da kwamitin bincike ya same shi da hannu a belin Sulaiman Aminu Danwawu, da ake zargi dillancin miyagun kwayoyi.

Wasikar ta bukaci Abubakar Sharada da ya mika dukkan kadarorin gwamnati da ke hannun sa ga babban sakataren harkokin siyasa (REPA), a ofishin SSG, kuma kada ya sake bayyana  kansa a matsayin jami’in gwamnatin Kano.

Hakazalika, gwamnan ya sauke Tasiu Adamu Al’amin Roba, babban mataimaki na musamman  bayan kama shi da laifin canza wa buhunan hatstin tallafi a Sharada a shekarar 2024.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *