An Kama Yahaya Bello

Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), ta kama Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, kan zargin karkatar da kuɗaɗe a lokacin gwamnatinsa.

Jami’an EFCC sun bayyana cewa suna  yi masa tambayoyi dangane da zarge-zargen da ake masa.

Sai dai wasu rahotanni na cewa Yahaya Bello ya je ofishin EFCC ɗin ne da kansa ba kamo shi aka yi ba.

Idan ba a manta ba Yahaya Bello, ya shiga wasan ɓuya tsakaninsa da EFCC tun bayan da ya sauka daga mulki.

Duk da zarge-zargen da EFCC ke masa na karkatar da kuɗaɗe a lokacin da yake mulkin Jihar Kogi, Bello ya musanta aikata hakan.

Post masu alaƙa

Sojojin Najeriya sun daƙile yunƙurin garkuwa da mutane tare da ceto mutum 23

Dan KAROTA da direba ya buge ya gudu Nasiru Abdullahi Mai Jihadi ya rasu ya bar mata 2 da ‘ya’ya 12.

An kama budurwa ‘yar shekara 15 kan safarar miyagun kwayoyi a Delta.