Ba za mu lamunci tada zaune tsaye ba a yayin tarukan siyasa—Tinubu

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su tashi tsaye wajen dakile duk wani yunkuri na masu tayar da tsaye da janyo da rikice-rikice a yayin tarukan siyasa yana mai cewa, gwamnatinsa ba za ta lamunci tashin hankali ba yayin da ake ci gaba da kamfen din zaben 2027.

Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin wani sakon gargadi na musamman da ya fitar wanda ya sanya wa hannu da kansa a ranar Juma’a, inda ya yi Allah-wadai da wasu hare-haren da aka kai a wasu tarukan siyasa a sassa daban-daban na kasar a baya-bayan nan.

Shugaban ya kuma yi kira ga ’yan siyasa da magoya bayansu da su guji duk wani nau’in tashin hankali a harkokin siyasa.

Post masu alaƙa

2027: Sarkin Gumel Alhaji Dr. Lawan Ahmad Muhammad Sani, Ya Tabbatar Wa Namadi Da Kuri’un Al’ummar Masarautar

Tinubu zai ƙaddamar da titin jirgin ƙasan Kaduna zuwa Kano a watan gobe

Atiku ya yi zargin ƙoƙarin hana shi takara a 2027 saboda kasancewarsa ɗan Arewa