Yar Gombe ta lashe gasar karatun Alƙur’ani ta duniya a Saudiyya

Maryam Ibrahim Dan’azumi, ’yar asalin Jihar Gombe, ta lashe gasar karatun Alƙur’ani ta Duniya karo na 46 da aka gudanar a ƙasar Saudiyya.

Maryam, ɗalibai ce a makarantar Abubakar Siddiq Community Islamic School for Qur’anic Memorisation da ke Gombe, ta wakilci Najeriya a gasar da aka gudanar a birnin Makkah.

Ta yi nasara ne a rukuni na haddar Alƙur’ani Mai Tsarki tare da karatu, bin ƙa’idojin Tajweed da tafsiri.

Maryam, ta zo ta farko a cikin abokan karawarta daga ƙasashe daban-daban, lamarin da ya sa ta zama abar alfahari a idon Gombawa da Najeriya.

Nasararta ta zama ta musamman saboda wannan ne karon farko da aka bai wa mata damar shiga gasar tun bayan fara ta shekaru 46 da suka gabata.

Kafin ta wakilci Najeriya a gasar ta duniya, Maryam, ta fara lashe matsayi na farko a matakin ƙaramar hukuma da na jihar, sannan ta lashe gasar a matakin ƙasa kafin a zaɓe ta, ta wakilci Najeriya a Saudiyya.

A baya an bayyana cewa Maryam ta samu kyautar Riyal dubu 3000 na Saudiyya, kwatankwacin kusan Naira miliyan 120, saboda nasarar da ta samu.

A halin yanzu, Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya taya Maryam murna kan wannan babbar nasara.

A cikin wata sanarwa da kakakinsa, Ismaila Uba Misilli, ya fitar, gwamnan ya ce nasarar Maryam abin alfahari ce ga Gombe da Najeriya baki ɗaya.

Ya kuma taya iyayenta, malamanta da al’ummar Musulmin Gombe murna.

Gwamnan ya ce nasarar Maryam ta nuna muhimmancin jajircewa, ladabi da dagewa wajen neman ilimi.

Ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa ilimin matasa, ciki har da karatun Alƙur’ani da sauran ilimin addini.

Gwamnan, ya ce yana sa ran tarbar Maryam tare da karrama ta idan ta dawo Najeriya, domin ƙarfafa mata gwiwa da kuma zaburar da sauran matasa, musamman ’yan mata.

Ya kuma yaba wa makarantar Abubakar Siddiq Community Islamic School for Qur’anic Memorisation saboda gudunmawar da ta bayar wajen horar da Maryam har ta kai ga wannan babban matsayi a duniya.

Post masu alaƙa

Gwamnatin Jigawa za ta haɗa gwiwa da Masar kan noman dabino da dankali

Miyagun kwayoyi: NDLEA ta kama mutum 80 a Kano

El-Rufai ya shigar da ICPC ƙara kan hana shi ganin iyalansa