An kashe shugabannin Miyetti Allah 7 cikin shekara 2

Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) ta tabbatar da kisan da aka yi wa shugabanta na jihar Kwara, Idrissu Abubakar cikin alhini.

A ranar Asabar ne wasu ‘ƴan bindiga ɗauke da makamai ne suka auka gidan shugaban ƙungiyar inda suka halaka shi.
Kisan shugaban Miyetti Allah na jihar Kwaran na zuwa ne kusan wata biyu bayan kashe shugaban ƙungiyar na jihar Katsina, Alhaji Sirajo Ahmad Mairana.

Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar mai ɗauke da sa hannun babban sakatarenta na ƙasa, Bello Aliyu Gotomo, ta yi Allah wadai da kisan da aka yi wa Idrissu Abubakar mai shekara 33.

Sanarwar ta ambato shugaban ƙungiyar na ƙasa, Baba Othman Ngelzarma na cewa an kashe Idrissu Abubakar da mislain ƙarfe 10:00 na daren da ya gabata bayan komawa gida daga sallar Tarawih.

Ƙungiyar ta ce cikin shekara biyu da suka gabata, ‘ƴan bindiga sun kashe shugabanninta bakwai na jihohi da na ƙananan hukumomi.

Post masu alaƙa

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC

Yan Sandan a Kano sun kama mutane 244, ciki har da 117 da ake zargi da fadan daba.

Ƴansanda sun ƙara tsaurara matakan tsaro a bikin Takutaha, tare da gargaɗin masu yunkurin tada zaune tsaye.