Home » An Naɗa Pantami Majidaɗin Daular Usmaniyya 

An Naɗa Pantami Majidaɗin Daular Usmaniyya 

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya naɗa Farfesa Isa Ali Pantami sarautar Majidadin Daular Usmaniya.

A ranar Asabar din da ta gabata ne dai Sarkin Musulmi ya halarci taron shekara-shekara na Gidauniyar Shaihu Usman Ibn Fodiyo karo na 11, inda Farfesa Pantami ya gabatar da maƙala mai taken “Hadin kai a matsayin Maganin Rashin Tsaro da Talauci: Darussa Daga Jagororin Jihadin Sakkwato”.

Bayan kammala maƙalar ne, Majalisar Sarkin Musulmi karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ta karrama tsohon Ministan Sadarwa da lambar yabo bisa irin gudunmawar da ya bayar a matsayinsa na jagoran addini da siyasa.

Sarkin Musulmi ya bayyana irin rawar da Pantami ke takawa a bangarori da dama da suka dace da abin da fadar mai Martaba Sarkin Musulmi ta sa a gaba kawo ci gaba da jin dadin al’umma.

Sultan Abubakar ya ce “Farfesa Pantami ya nuna jajircewarsa wajen inganta rayuwar ‘yan Najeriya. Babban gudunmawar da ya bayar ta fi ƙarfi a fannin ilimi, hidimar jama’a, da ci gaban al’umma abin yabawa ne,”

“Kokarin da ya yi na bayar da tallafin karatu ga daliban da ba su da galihu da kuma samar da guraben ayyukan yi ga kwararrun matasa ya yi tasiri sosai ga jama’ada dama”.

Majalisar Sarkin Musulmin ta bayyana fatan cewa wannan karramawar za ta zaburar da sauran jama’a wajen gudanar da aiki irin na Farfesa Pantami.

Sakataren gwamnatin jihar Sokoto, Bello Sifawa, wanda ya wakilci gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya bayyana godiyarsa ga majalisar Sarkin Musulmi bisa karramawar da aka yi wa Pantami.

Fafesa Pantami ya godewa mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Abubakar Sa’ad tare da alkawarin ci gaba da gudanar da ayyukansa da ya saba.

Tsohon Ministan ya bukaci daukacin ‘yan Najeriya da su hada kai wajen samar da kyakkyawar makomaga al’ummar kasar.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?