An Sace Amarya A Sakkwato

Wasu ’Yan Bindiga dauke da muggan makamai sun sace wata amarya da ƙwayenta huɗu a Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato ranar Asabar. 

‘Yan bindigar sun sace amaryar da kawayenta ne a garin Kwaren Gamba, da ke yankin Kuka Teke.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wannan kauye na fama da hare-hare daga yaran kasurgumin dan ta’addan nan Bello Turji.

Wadan da suka shaida faruwar lamarin  sun ce ‘yan bindigar sun afka wa yankin sannan kuma tafi da waɗanda abin ya shafa, lamarin da ya jefa tsoro da tashin hankali a zukatan mazauna yankin.

 

Post masu alaƙa

Gwamnatin Kwara ta haɗa mutum 146 da aka sace a Woro da iyalansu

Tinubu ya nemi kotu a Amurka ta hana fitar da takardun zarginsa da safarar ƙwaya’

Tinubu da gwamnoni sun kafa kwamitin lalubo hanyoyin rage tsadar sufuri