Home » ‘Yan Sanda Na Farautar Sanusi Bature Dawakin Tofa

‘Yan Sanda Na Farautar Sanusi Bature Dawakin Tofa

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Rahotanni na cewa Akalla jami’an ‘yan sanda 40 na musamman ne ke farautar mai magana da yawun gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature Dawakin-Tofa.

An ce mukaddashin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Dokta. Abdullahi Umar Ganduje ne ya kai ƙarar Sanusi Bature bisa zargin cewa shi ya kitsa dakatar da shi daga jam’iyyar APC a mazaɓarsu kwanakin baya.

Ana zargin cewa ‘yan sandan da aka turo daga Abuja domin kama Sanusi Bature Dawakin-Tofa suna zaune ne a babban otal ɗin Tahir makonni biyu da suka gabata domin aiwatar da wannan umarni.

Wata majiya daga iyalan Sanusi Bature sun shaida wa manema labarai a ranar Talata cewa, tawagar jami’an ‘yan sandan da ke sanye da fararen kaya a kusa da gidan su a ranar Litinin.

Daya daga cikin na kusa da Sanusi da ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro ya koka kan yadda jami’an tsaron sirrin suka yi ta zuwa gidan har sau biyar.

Kawo lokacin hada wannan rahoto duk ƙokarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ci tura, kamar yadda jaridar Nigeriantracker ta wallafa

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?