Hukumar kididdiga ta Najeriya (NBS) ta ce aƙalla ana sa ran an kashe ‘yan Najeriya dubu 614, 937 yayinda aka yi garkuwa da wasu dubu 2,235,954 a fadin kasar tsakanin watan Mayun 2023 zuwa Afrilu 2024
NBS ta bayyana hakan ne a jiya Talata a cikin rahotonta mai suna ‘The Crime Experienced and Security Perception Survey (CESPS) 2024’.
Rahoton ya tabbatar da cewa an yi garkuwa da ‘yan Najeriya miliyan biyu da dubu ɗari biyu a fadin kasar yayin da aka biya Naira tiriliyan biyu da dubu ɗari biyu a matsayin kudin fansa.
- Gwamnatin Jigawa Na Asarar Naira Miiliyan 314 Duk Wata Kan Ma’aikatan Bogi 6,348
- ‘Yan Sanda Sun Kama ‘Yan Daba 24 Da Muggan Makamai A Kano
Bayanin na NBS y ce, aƙalla duk ɗan Najeriya guda da aka sace ba a sake shi ba sai da aka biya masa Naira Miliyan biyu da dubu ɗari bakwai (2.7).
Hakazalika rahoton ya bayyana cewa an fi samu kisan ne a yankunan karkara inda ake hasashen an kashe kimanin mutane 335,827 yayin da aka kashe kimanin 279,110 a manyan biranen Najer.
Masana dai na ganin cewa duk da cewa akwai manyan mutane da aka sace, amma talakawan kauyuka ne suka fi shan wahala.
Rahoton shiyya-shiyya ya nuna cewa a Arewa maso Yammacin Najeriya ne aka fi kashe mutane, ina aka ce an kashe mutum dubu ɗari biyu da da ɗari shida da talatin (206,030), yayinda aka kashe mutane dubu ɗari da tamanin da takwas da ɗari tara da cas’in da biyu (188,992) a Arewa maso Gabas.
Rahoton ya nuna cewa an samu kashe-kashe a kudancin Najeriya inda ya fi ƙaranci kuma shi ne kudu maso Yamma, inda aka gano an kashe mutane dubu goma sha biyar da ɗari shida da cas’in da uku(15,693).