An Saka Dokar Hana Fita A Mina Jihar Neja

Gwamnan Neja Umar Mohammed Bago, ya saka dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 12 a Minna babban birnin Jihar.

An ɗauki wannan matakin ne sakamakon hare-haren da suka janyo salwantar rayuka.

A jawabin dokar, gwamnan ya ce, an haramta zirga-zirgar baburan ’yan acaɓa da masu Keke Napep daga ƙarfe 6 na yamma zuwa 6 na safe.

Gwamnan ya bayyana hakan a yayin wani taro na musamman da ya gudanar da masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro da ya ƙunshi sarakunan gargajiya da shugabannin hukumomin tsaro a Fadar Gwamnatin jihar a ranar Talata.

Sai dokar ba ta shafi duk wata buƙatar lafiya ta gaggawa ba, Bago ya ce ba a buƙatar ganin ababen hawa daga lokacin da dokar ta fara aiki.

Ya ce ya ɗauki wannan matakin ne da zummar daƙile matsalar tsaro da babban birnin ke fuskanta.

Bago ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta zuba ido a yayin da marasa son zaman lafiya ke ci gaba da kai hare-hare da kashe mutanen da ba su ji ba kuma ba su gani ba a jihar.

Gwamnan ya umarci dukkan dagatai da masu unguwanni da su tabbatar da ɗaukar bayanan duk wasu baƙi da suka shigo yankunansu.

Haka-zalika, ya yi gargaɗin cewa duk gidan da aka kama yana bai wa ‘yan tada zaune tsaye mafaka ko masu fataucin muggan ƙwayoyi za a rushe shi.

Post masu alaƙa

Hadejia ta cika shekaru 120 da cin nasara kan turawan mulkin mallaka na Birtaniya.

NSCDC ta rufe wani gida da ake zargin ana safarar jarirai a Legos.

Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta kama wanda ake zargi da safarar Alburusai a tankin Babur