A ranar 17 ga watan da ya gabata ne, gwamnatin jihar ta ja hankalin al’umma kan ɓarkewar cutar ta kwalara a Ijebu da ke Arewacin jihar.
Majiyarmu ta rawaito mana cewa wannan annoba ta kuma yaɗu zuwa Arewaci da Kudancin ƙananan hukumomin Abeokuta da ke babban birnin.
A yayin da kwamishiniyar lafiya ta jihar, Dr. Tomi Coker, ke ƙarin haske kan wannan al’amari, ta tabbatar da faruwar da ɓarkewar cutar tare da samun rahotannin cewa kusan mutane ɗari biyu da arba’in da shida sun kamu da cutar.
kwamishiniyar lafiyar ta ce abubuwa da yawa ne suka sabbaba faruwar lamarin da ya haɗa da yawan bayan gida a sarari barkatai da rashin ingantaccen tsari na kula da datti da hanyar samun tsabtataccen ruwa.
Ta ce tuni gwamnatin jihar ta soma yin amfani da sinadarin Kulorin domin kashe ƙwayoyin cutar ta hanyar zuba wa rijiyoyin da ke Ijebu wacce ita ce ƙaramar hukumar da abin ya fi tsamari.
Sannan ta shawarci al’umma kan su guje wa yin bayan gida a sarari tare da ƙoƙarin gina banɗakuna da haƙa rijiyoyi a gidajensu.
Sannan ta yi kashedin cewa, gwamnati za ta fara bi gida-gida domin tabbatar da an samar da baɗaki, kuma akasin hakan zai iya jawowa gwamnati ta ƙwace gidan ko yin hukunci mai tsanani.