An Samu Raguwar Ta’addanci A Arewacin Nijeriya : Nuhu Ribadu

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya ce an samu raguwar hare-haren Boko Haram da na ƴanbindiga har ma da rikice-rikice tsakanin al’ummomi a yankin arewacin ƙasar cikin shekaru biyu da suka wuce karkashin gwamnatin shugaba Tinubu – idan aka kwatanta da gwamnatin da ta gabata.

Ya bayar da misalin cewa an kashe mutum 1,192 sannan an sace sama da 3,348 a jihar Kaduna a gwamnatin da ta shuɗe, yayin da sama da mutane 5,000 suka rasa rayukansu a jihar Benue a wannan lokaci.

Ribadu ya bayyana haka ne a yau Talata yayin jawabi a taron masu ruwa da tsaki na arewacin Najeriya wanda aka gudanar a jihar Kaduna.

Ya ce nasarar da aka samu a yaƙi da rashin tsaro ya samo asali ne sakamakon umarnin da shugaba Tinubu ya bai wa jami’an tsaro kan bin tsarin tabbatar da tsaro na bai-ɗaya.

Ya ƙara da cewa an samu nasarar sakin mutum 11,259 waɗanda aka yi garkuwa da su a watan Mayu kaɗai – a wasu samame daban-daban da sojojin Najeriya suka kai a arewa maso yamma.

Ribadu ya kuma bayyana cewa jami’an tsaro sun kashe shugabannin ƴanbindiga da mambobinsu da dama a jihohin Zamfara da Kaduna da kuma Katsina.

Mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan tsaro ya yaba wa gwamnan jihar Kaduna Uba Sani kan amfani da hanyoyi daban-daban wajen shawo kan matsalar tsaro a kudancin jihar da Birnin Gwari har ma da wasu yankuna da ke fama da matsalar tsaro a faɗin jihar.

Post masu alaƙa

Zauren haɗin kan malamai ya buƙaci gwamnatin Kano ta tsawatarwa ƴan daba da masu saka su.

NNPCL ya ƙulla yarjejeniyar gyara matatun man fetur na Warri da Fatakwal

Juyin mulki: Mutum 2 sun amince sun san da shirin kifar da gwamnati