Kungiyar Malaman Jami’ar jihar Yobe Ta Janye Yajin Aiki

Ƙungiyar malaman jami’a reshen jami’ar jihar Yobe sun sanar da janye yajin aiki da suka shiga ranar 11 ga watan Yulin, 2025.

Shugaban malaman jami’ar, Ahmed Karange, ya bayyana cewa sun cimma yarjejeniya da gwamnatin jihar ta Yobe, inda ta yi alkawarin biyan sauran buƙatu da malaman ke nema.

“Bayan cimma yarjejeniyar, shugaban malaman jami’ar ya bayar da damar janye yajin aikin,” kamar yadda sanarwar da suka fitar ta bayyana.

Sanarwar ta buƙaci dukkan mambobi da su koma bakin aiki nan take

Post masu alaƙa

Ƴansanda sun ƙara tsaurara matakan tsaro a bikin Takutaha, tare da gargaɗin masu yunkurin tada zaune tsaye.

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 26 a Borno

Tinubu ya tafi hutun mako uku