Darakta-Janar na Cibiyar Kula Tattalin Arziƙin Yammacin Afirka, WAIFEM, farfesa Baba Yusuf Musa, ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta mai da hankali wajen samar da ƙarin kuɗin shiga domin magance ƙalubalen tattalin arziƙi da ƙasar nan ke fuskanta.
Ya bayyana hakan ne a cikin takardar da ya gabatar a yayin taron Hukumar Ba da Lamuni da Bankin Duniya a Marrakech da ke ƙasar Morocco.
Ya ce gwamnatin tarayya na da damammaki da za ta iya ƙara yawan harajin da take samu.
Ya ce sanya harajin kan kadarori hanya ce da gwamnatin za ta samu ƙarin haraji, domin kaso ɗaya cikin ɗari kaɗai na haraji ake samu daga kadorori a ƙasar nan.
Ya ba da misali da ya kamata a riƙa karɓar haraji a kan mutane da ke ba da gidajensu haya.
Amma kafin gwamnatin ta yi hakan, akwai buƙatar yin rajistar masu kadarori da kuma wani tsari na nazarinsu a ƙarshen kowacce shekara.
Sannan ya shawarci gwamnatin tarayya da ta zamanantar da hanyar karɓar haraji saboda ƙorafi da ake yi game da tsarin biyan a yanzu.
Ya kuma buƙaci ‘yan Najeriya da su nuna juriya game da halin da za a iya samun kai sakamakon sabbin dokoki da sabuwar gwamnatin Tinubu za ta kawo da ka iya kawo tsadar rayuwa a yanzu.