Kotun Ƙoli Ta Tabbatar da Sanata Rufa’i Sani Hanga a Matsayin Zaɓaɓɓen Sanata

Kotun kolin nijeriya ta tabbatar da sanata rufa’I sani hanga a matsayin zabbaben sanatan kano ta tsakiya a jam’iyar NNPP.

Kotun kolin bisa jagorancin  mai shari’ah uwani abba aji, ta gudanar da hukuncin ne a yau jumu’ah , inda ta ayyana sanata rufa’I sani hanga  a matsayin wanda ya lashe  zaben na sanatan kano ta tsakiya a jami’iyar NNPP.

Kwankwaso tare da zababbbun ‘yan majalisun tarayya na jam’iyyar NNPP

  Da yake Karin haske game da hukuncin lauyan jami’iyyar ta NNPP barista Bashir tudun wazirci yace kotun kolin ta jaddada hukuncin baya na kotun tarraya .

Hukumar zabe mai zaman Kanta inec ta dai bayyana  malam Ibrahim shekaru a matsayin wanada ya lashe zaben na sanatan kano ta tsakiya, lamarim da ya kawo cecekuce tsakanin yan jami’iyar ta NNPP.

Post masu alaƙa

Jigawa Za Ta Bai Wa Alhazai Abinci Sau Uku a Rana a Hajjin 2026

Namadi Ya Kaddamar da Shirin Fadada Ilimi yayin da SLU ta Yaye Dalibai Sama da 4,000

Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Jigawa Ta Taya Gwamna Namadi Da Musulmi Murnar Eid-el-Fitr