Zabe

ADC ta fitar da sunayen ’yan takarar gwamnanta a jihohi 28

Jam’iyyar ADC ta fitar da sunayen ’yan takararta na gwamna da mataimakin gwamna a jihohi 28 domin tunkarar zaɓen 2027. Jerin ya ƙunshi wasu fitattun ’yan siyasa, ciki har da tsohon ɗan takarar gwamnan Kaduna na PDP, Isa Ashiru, tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami. Sauran sun haɗa da tsohon ɗan takarar gwamnan Delta, Great Ogboru, […]

Read more

Zaɓen cike gurbi: Rundunar ƴan Sandan jihar Kano ta taƙaita zirga-zirga a Dawakin Kudu da Warawa.

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano ta bayyana matakan tsaro da aka amince da su gabanin zaben cike gurbin ɗan majalisar Tarayya mai wakiltar Dawakin Kudu da Warawa wanda zai gudana ranar Asabar. Wannan na ƙunshe cikin wata sanarwa da kakakin rundunar,CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar Yace bisa umarnin kwamishinan yan sandan jihar Kano,  CP […]

Read more

Tinubu ya yaba wa gwamnonin APC kan zaɓen fitar da gwani

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana gamsuwarsa kan yadda ya ce gwamnonin ƙasar sun shirya tare da gudanar da zaɓukan fitar da gwani a faɗin jihohisu. Yayin da yake jawabi a mazaɓarsa ta Ikoyi bayan ya halarci zaɓen, Shugaba Tinubu ya ce ya ji daɗin yadda zaɓen ke tafiya cikin lumana kamar yadda aka tsara. […]

Read more

PDP ta shirya lashe zaɓukan 2027 – Tanimu Turaki

Shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, Kabiru Tanimu Turaki, ya bayyana shirin jam’iyyar tasu na yin nasara a babban zaɓen 2027. Turaki na magana ne bayan ganawarsa da tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo a Abeokuta babban birnin jihar Ogun yau Asabar. Obasanjo ne shugaban ƙasa na farko ƙarƙashin PDP a 1999 kuma ɗaya […]

Read more