An Tsinci Gawar Wani Barasaken Gargajiya A Filato

Wata ƙungiyar Cigaban Kanam (KADA) ta fitar da sanarwar alhini da fushi kan kisan gillar da aka yi wa shugaban unguwar Shuwaka, Malam Hudu Hassan Barau, wanda aka fi sani da Sarkin Shuwaka daga yankin Kyaram, al’ummar Garga a Karamar Hukumar Kanam ta Jihar Filato.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a yau Litinin

Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi garkuwa da shi kusan kwanaki shida da suka wuce, inda daga bisani aka kashe shi, kuma aka gano gawarsa a Dajin Wanka a safiyar Litinin 15 ga Satumba, 2025.

A cikin sanarwar, ƙungiyar ta ce wannan ɗanyen aiki ya sake tunasar da matsalar tsaro da ta daɗe tana addabar yankin.

Ƙungiyar ta zargi gwamnati a matakai daban-daban da gazawa wajen ɗaukar matakan da suka dace don shawo kan hare-haren ‘yan bindiga da suka jefa al’ummar Garga da kewaye cikin tsoro da fargaba.

Ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnan Jihar Filato, Barr. Caleb Mutfwang, da ya ayyana dokar ta-ɓaci a yankin Garga tare da tura jami’an tsaro da za su iya tunkarar matsalar.

“Haka kuma muna roƙon Sanata mai wakiltar Filato ta Tsakiya, Sanata Diket Plang, da ya yi amfani da kujerarsa wajen kawo ɗauki daga gwamnatin tarayya tare da kai gaggawar tallafi ga ɗaruruwan mutanen da abin ya shafa.” in ji ƙungiyar

Sanarwar ta kuma caccaki ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Pankshin da Kanke da Kanam, Yusuf Adamu Gagdi, bisa abin da ta kira shiru da rashin ɗaukar mataki kan kashe-kashe a Kanam.

“Muna kira ga ɗan majalisar jiha daga mazabar Kantana, Hon. Samila Bala Nomada da ya haɗa kai da gwamnati wajen ganin an ba da kuɗade da tallafi domin tsaron mazaɓarsa.” in ji sanarwar.

Ƙungiyar ta ce ba za ta sake jurewa da shiru da halin ko-in-kula na shugabanni ba, inda ta buƙaci a kawo adalci da tsaro ga al’ummar Garga da Kanam baki ɗaya.

BBCH

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda