Rundunar Yan Sandan Kano Ta Sasanta Asibitin AKTH Da KEDCO

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta shiga tsakani don sasanta rikicin da ya ɓarke tsakanin Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki shiyyar Kano (KEDCO).

Rikicin ya samo asali ne daga katse wutar lantarki da asibitin ya zargi KEDCO da yi, inda ya ce hakan ya kawo cikas ga aiyukan lafiya masu muhimmanci a asibitin, ciki har da zargin mutuwar marasa lafiya.

Sasantawar da Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya jagoranta ta biyo bayan zarge-zargen cewa katsewar wutar ta haddasa mutuwar wasu marasa lafiya da ke kan na’urar taimakon numfashi a asibitin.

Sai dai KEDCO ya musanta zargin a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, yana mai cewa asibitin na kokarin bata sunan KEDCO ne kawai.

A cewar mai magana da yawun ‘yan sandan jihar  Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an gudanar da taron sasancin ne a shelkwatar ‘yan sandan  dake Bompai, inda aka zauna da Shugaban asibitin, Farfesa Abdulrahman Abba Sheshe, da Shugaban KEDCO, Abubakar Shu’aibu Jimeta.

Taron ya mayar da hankali ne kan warware tankiyar da kuma dawo da wutar lantarki ga asibitin, wanda ke ya fuskanci matsaloli sakamakon katse wutar.

Sanarwar ta ce, “Bangarorin biyu sun nuna godiya ga matakin gaggawa da ‘yan sanda suka dauka, KEDCO ya amince da dawo da wutar lantarki nan take, inda alamu ke nuna cewa rikicin ya zo karshe.”

Kiyawa ya kara da cewa, “Rundunar ‘Yan Sanda ta jaddada kudirinta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da tabbatar da ci gaba da aiki ba tare da tangarda ba a bangaren kiwon lafiya.”

Sanarwar ta kuma ce kwamishinan ‘yan sanda ya yaba wa asibitin AKTH da kuma  KEDCO bisa hadin kai, tare da alkawarin ci gaba da goyon baya don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda